Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami mai linzami

A yau Juma’a, Koriya ta Arewa ta yi gwajin wani sabon makami mai linzami wanda kuma ke kakkabo jirgin sama, a daidai lokacin da Kwamintin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke shirin gudanar da zama domin mayar da martini ga Koriyar.

Sabon gwajin na zuwa ne  gabanin zaman Kwamitin Tsaron na Majalisar Dinkin Duniya domin nazari kan wani gwajin na dabam da Koriya ta Arewar ta yi a farkon makon nan, lamarin da ya haddasa kumfar baki.

Makamin da Koriyar ta harba a yau, na da gagarumin karfin yaki, baya ga wasu sabbin fasahohi da aka makala masa kamar yadda Kamfadin Dillancin Labaran Kasar ya rawaito.

Wani hoto da Jaridar Rodong Sinmun ta wallafa ya nuna makamin mai linzamin na lulawa can sararin samaniya bayan an cilla shi daga cibiyarsa.

Wannan dai na a matsayin takala ta baya-bayan nan da Koriyar ta yi bayan sassaucin da ta yi domin ganin kamun ludayin gwamnatin shugaba Joe Biden na Amurka.

A ranar Larabar da ta gabata, shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un ya caccaki bukatar Amurka ta shiga tattaunawa ba tare da shimfida ka’idoji a matakin farko ba, abin da ya bayyana a matsayin wayo.

Leave a Reply

Your email address will not be published.