Etebo zai yi jinyar watanni biyar saboda mummunan rauni

Dan wasan Najeriya mai taka leda a Watford ta Ingila, wato Peter Etebo zai yi zaman jinyar watanni biyar saboda raunin da ya samu a cinyarsa kamar yadda kungiyarsa mai buga gasar firimiya ta sanar.

Etebo mai shekaru 25 wanda ya koma Watford a matsayin aro daga Stoke City, ya samu raunin ne a wasan da Watford ta yi canjarsa 1-1 da Newcastle a karshen makon da ya gabata.

Tuni aka fara hasashen cewa, wannan raunin nasa, ka iya hana shi halartar gasar cin kofin Afrika da kasar Kamaru za ta karbi bakwanci a cikin watan Janairu mai zuwa.

Kocin Watford Xisco Munoz ya ce, lallai wannan raunin na Etebo ya bakanta masa rai, abin da ya bayyana a matsayin babbar matsala a gare su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *