Dan majalisar tarayya na cikin masu daukar nauyin Kanu da Igboho-Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, wani dan majalisar tarayyar kasar na cikin gungun mutanen da ke daukar nauyin Nnamdi Kanu da Sunday Igboho wadanda ke rajin ballewa daga kasar.

Shugaba Buhari ya ce, binciken da ake kan gudanarwa ya nuna cewa, wasu fitattun masu hannu da shuni na daukar nauyin Kanu da Igboho da ke hannun jami’an tsaro.

Muna bibiyar wadannan masu hannu da shunin sau da kafa da suka hada da wani mamba a majalisar tarraya” inji Buhari

Shugaba Buharin ya fadi haka ne a yayin gabatar da jawabinsa kan cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yanci daga Turawan Mulkin Mallaka na Birtaniya.

Shugaban ya bayyana bikin samun ‘yancin kan a matsayin wanda ke hada kan al’ummar Najeriya masu mabanbantan kabilu da addinai.

A cewarsa, daukacin al’ummar kasar sun dunkule wuri guda a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960, lokacin da yankunan Gabashi da Yammaci da Arewacin kasar suka hadu domin bikin murnar samun ‘yancin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.