UEFA ta haramtawa Wan-Bissaka buga wasanni 2 na gasar zakarun Turai

Hukumar UEFA ta haramtawa dan wasan baya na Manchester United, Aaron Wan-Bissaka buga wasanni biyu na gasar zakarun Turai.

An dai kori Wan-Bissaka a minti na 35 ne a yayin wasan da Manchester United ta sha kaye a hannun Young Boys da kwallaye 2-1 a karawar su ta farko cikin gasar cin kofin zakarun Turai ta bana, saboda laifin da ya yi na yi wa Christopher Martins Pereira da ke tawagar ta Young Boys mugunta.

Da fari dai jan kati kawai aka baiwa Wan-Bissaka abinda ke nufin zai rasa wasa daya, amma daga bisani UEFA ta kara haramcin zuwa wasanni biyu.

Hukuncin na nufin Wan-Bissaka zai rasa buga wasan da Man United za ta yi da Atalanta a ranar 20 ga watan Oktoba, ban da wasan ranar Laraba 29 ga watan Satumba da bai buga ba, wanda suka samu nasara kan Villarreal da kwallaye 2-1.

Leave a Reply

Your email address will not be published.