Karon farko, Hotunan Mata sun yi fareti a bikin tunawa da ranar Saudiyya

Karon farko a tarihin Kasar Saudiyya, mata a kasar Saudiyya sun yi musharaka a bikin tunawa da ranar kafa kasar ta Saudiyya.

Ana murnar ranar Saudiyya ne kowace 23 ga Satumba shekara domin murnar ranar da aka canza sunan kasar daga Masarautar Najd da Hijaz zuwa Masarautar Saudiyya.

A cewar Wikipedia, tsohon Sarkin Saudiyya Abdul Aziz Al Saud ne yayi hakan a shekarar 1932.

Sannan a 2005, Sarki Abdullah ya alanta ranar matsayin ranar murna ga al’ummar kasar.

Ana bukukuwa a ranar da wakoki, rawa, faretin Sojoji, da faretin jiragen sama.

Tun da aka fara murnar ranar a 2005, wannan shine karo na farko da mata zasuyi musharaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *