Za’a sanar da sunayen wadanda suka cancanci lashe kyautar Ballon d’Or

Masu shirya bata da kyautar Ballon d’Or da ake baiwa gwarzon dan kwallon kafar da ya yi fitce a shekara, sun ce za’a bada kyautar a ranar 29 ga Nuwamba a birnin Paris na kasar Faransa.

Mujallar ta Faransa dake bada kyautar tace, a ranar 8 ga watan Oktoba za a bayyana sunayen wadanda za a zaba don basu da kyaututtukan, wadanda suka hada da gwarzon dan wasa na Maza da na Mata, da na bangaren matashin dan wasa da kuma golan da yayi fitce a shekara.

Lionel Messi da lashe kyautar har sau shida da Megan Rapinoe suka lashe lambobin yabon na ƙarshe s shekarar 2019.

An soke taron shekarar da ta gabata saboda barkewar cutar coronavirus.

Baya ga kyautar FIFA ta kwannan nan, Ballon d’Or, wanda Stanley Matthews ya fara karba a shekarar 1956, ya kasance ɗaya daga cikin kyaututtukan mafi girma da daraja a fannin wasannin ƙwallon ƙafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *