WHO ta daura aniyar murkushe cutar sankarau nan da 2030

Hukumar Lafiya ta Duniya ta gabatar da wani shiri a yau laraba, wanda ta ce a karkashin sa za ta shawo kan cutar sankarau nan da shekarar 2030, ta hanyar rage yawan mutane akalla dubu 250,000 da cutar ke kashewa a duk shekara.T

Lokacin da take kaddamar da sabbin matakan da ta tsara don cimma burin na kawar da cutar ta Sankarau, hukumar ta WHO ta ce tana fatan rage adadin masu kamuwa da cutar da kuma rage mace –macen da take haddawa da kashi 70 cikin 100.

Shugaban hukumar lafiyar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce lokaci ya yi da za a shawo kan cutar sankarau a duniya baki daya ta hanyar hanzarta fadada amfani da kayan aikin da ake da su da suka hada da alluran rigakafi, jagorantar sabon bincike da karfafan binciken ganowa da magance dalilai daban -daban da suke haddasa cutar, sai kuma baiwa wadanda cutar ta sankarau ta shafa kulawa ta musamman.

Sankarau dai cuta ce da ke haddasa kumburi a ganuwar da ta kewaye kwakwalwar dan adam da kashin baya, galibi sanadiyyar kamuwa da kwayoyin cuta, lamarin da kan sanya ta zama annoba mai saurin yaduwa.

Binciken kwararru ya nuna cewar Sankarau na kashe akalla mutum daya daga cikin 10 da suka kamu da ita, galibinsu yara da matasa, yayin da take barin Hakanan akalla mutum 1 daga cikin biyar tare da nakasa tsawon lokaci, kamar farfadiya, raguwar karfin ji da gani, maatsalar jijiyoyi da akuma raunin kwakwalwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *