Taliban za ta yi amfani da sarautun gargajiya wajen tafiyar da mulki

Kungiyar Taliban ta sanar da shirin fara amfani da tsarin sarakunan gargajiya na wucin gadi, tsarin da kasar ke amfani da shi a shekarar 1964 wanda ya baiwa mata damar kada kuri’a kodayake ya yi togiya ga wasu hakkokin matan a batutuwa da dama.

Sanarwar fara amfani da kundin tsarin mulkin na 1964 da ke baiwa sarakunan gargajiya karfin iko wanda aka fi sani da kundin sarki Mohammad Zahir Shah tun a yammacin jiya talata ministan shari’ar na Taliban Mawlavi Abdul Hakim Sharaee ke sanar ad shirin fara amfani da shi.

A jawabin da ya yi kan fara amfani da kundin na Sarki Shah ministan ya ce sarakunan gargajiyar za su tafiyar da mulki bisa tanadin shari’ar Islama yayinda kungiyar za ta sanya idanu kansu tare da hukunta wadanda suka kaucewa tsari ko kuma tanade-tanaden da ke cikin kundin na sarki Mohammad Zahir.

Tun gabanin mamayar kasashen Duniya a kasar, Afghanistan na amfani da tsarin gargajiya wanda Sarki Mohammad Zahir Shah ya gabatar a shekarar 1963 gabanin hambarar da shi a shekarar 1973 tare da koma wani tsari daban.

Kundin tsarin na sarki Shah, shi ne na farko a tarihin Afghanistan da baiwa mata damar kada kuri’a da kuma damawa da su a harkokin siyasa baya ga basu damarmaki daban-daban a harkokin rayuwar yau da kullum.

Taliban wadda ta kwace iko da mulkin Afghanistan a watan Agusta, duk da alkawuran da ta dauka na sassauci tare da sauya salon kamun ludayi daga mulkinta na 1996 zuwa 2001, lamurra sun fara sauyawa bayanda suka fara hana mata aiki da karatu dama fita barkatai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *