Sojin Guinea sun gabatar da daftarin shirin mika mulki ga farar hula

Gwamnatin sojan da suka yi juyin mulki Guinea ta kaddamar da daftarin shirye-shiryen mayar da kasar kan mulkin farar hula. Kundin daftarin da aka bayyana ta kafar talabijin din kasar ya tsara jerin ayyukan, da suka hada da tsara sabon kundin tsarin mulki da kuma gudanar da sahihin zabe, to sai dai babu karin bayani kan lokacin da za a aiwatar da zaben.

Daftarin wanda aka karanta a gidan talabijin na kasar, ya bayyana ka’idoji da dama, ciki har da yin gyara ga kudin tsarin mulkin kasar, tare da tabbatar shirya ingantaccen zabe, duk da cewa daftarin bai bayyana yaushe ne za’a mika mulkin a hannun farar hula ba.

A ranar 5 ga wannan watan ne, sojoji a karkashin jagorancin kanal Mamady Doumbouya suka kame tsohon shugaban dan shekaru 83, Alpha Conde wanda ya yi ta fama da boran al’umma.

Conde, shi ne shugaban demokradiya na farko da kasar ta Guine ta yi, inda ya lashe zabe a shekarar  2010 da 2015, yayinda ya fara samun babbar matsala tun bayan yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska a bara.

Karkashin gyaran da Conde ya yiwa kundin tsarin mulkin kasar ya samu damar sake tsayawa takara a karo na 3 a shekarar 2020, lamarin da ya tunzura al’ummar kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *