Napoli na shirin hana Osimhen shiga gasar AFCON mai zawa

Napoli na shirin dakatar da dan wasan Super Eagles Victor Osimhen da sauran ‘yan wasan Afirka daga buga gasar cin kofin Afirka ta 2021 a watan Janairu mai zuwa a Kamaru.

A cewar jaridar Corriere dello Sport, Lauyoyin Napoli suna nazarin yuwuwar toshe manyan taurarin na Afirka ciki har da Osimhen daga wasannin na AFCON a shekara mai zuwa.

Napoli tana da ‘yan Afirka guda uku bayaga Osimhen, ciki harda Zambo Anguissa dake tawagar Kamaru mai masaukin baki, sai kuma Kalidou Koulibaly na Senegal da Adam Ounas, Ghoulam na Algeria.

AFCON wanda aka shirya gudanarwa a shekarar 2021 an canza shi zuwa 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga Fabrairu, 2022 saboda barkewar COVID-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *