Korea ta Arewa ta yi gwajin wani hatsabibin makami mai linzami

Korea ta Arewa ta yi gwajin wani sabon makami mai linzami da ke da matukar hadari, abinda ake ganin wani ci gaba ne ga fannin kere-kere a kasar dake da makaman Nukuliya.

Ana dai ganin wannan wani babban ci gaba ne ga kasar ta fannin tsaron kanta da kuma kange kanta daga duk wata barazana daga wasu kasashen.

Shi dai wannan sabon makami mai linzami dake da tsananin karfi da gudu, masana sun yi ittifakin cewa saurin sa ya fi na sauti sau biyar, wanda ake ganin ya sha kan duk wani kamami mai linzami, indai batun gudu ne.

Wannan dai na zuwa ne dai-dai lokacin da kasar Amurka ke kashe biliyoyin daloli wajen hana kasar kera wannan makami.

Makamin da aka yi masa lakabi da Hwasong-8 an yi gwajin nasa ne a lardin Jagang karkashin sanya idanun jagoran tawagar masu kera makamin Pak Jong Chon.

Sai dai har yanzu hukumomi basu bayyana irin nisan zangon da makamin zai iya yi ba, da kuma fadin murabba’in kasar da zai iya mamaye wa, bayanan da bisa al’ada hukumomi ke bayyanawa bayan sa’a guda da yin gwajin makamin.

Ana dai ganin Korea ta arewan na samar da makaman ne a wani salo na rige-rigen mallamar makamai masu hadari a duniya tsakanin ta da makwaftanta irin su Japan da China, dama kasashen yankin Asian baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *