Kazamar arangama ta hallaka dakarun gwamnati da ‘Yan tawayen Yemen akalla 100

Akalla ‘yan tawayen kasar Yemen da dakarun gwamnati 100 aka kashe a cikin sa’o’i 48 da suka gabata yayin da ake ci gaba da gwabza fada a birnin Marib mai muhimmanci ga bangorin biyu.

Majiyoyin soji da na kiwon lafiya sun bayyana cewar, dakarun kawancen da Saudiya ke jagoranta sun kai wasu jerin hare-hare ta sama kan ‘yan tawayen Huthi da Iran ke marawa baya, wadanda suka kara kaimi wajen kai farmaki kan Marib, birni na karshe da gwamnati ke da karfi.

A cewar majiyoyin, rikicin na baya-bayan nan ya yi sanadiyar hallaka ‘yan twayen na Huthis 68 da kuma dakarun gwamnatin Yemen 32.

Ba kasafai ‘Yan tawayen Huthis ke bayyana asarar rayukan baraden su ba,  to sai dai, tashar su ta Al-Masirah ta ba da rahoton kusan hare-haren jiragen sama na dakarun kawance 60 a birnin na Marib cikin kwanaki biyun da suka gabata.

An kashe daruruwan mayaka a wannan watan bayan da ‘yan tawaye suka sabunta farmakin neman kwace iko da babban birnin lardin mai arzikin man fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *