FG ta ayyana Juma’a 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu don murnar shekaru 61 da samun ‘yancin kai.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.

Ministan ya taya al’umman Najeriya murnar shekaru 61 da samun ‘yancin kai sannan ya tabbatar da jajircewar gwamnati wajen magancewa tare da kawar da duk wasu kalubale da dukkan matsaloli da ke addabar kasar.

Kalaman Aregbesola na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren din-din-din na ma’aikatar cikin gida, Dr Shuaib Belgore, a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Yace:

“Halinmu na kauna da iya tarban baki da kuma tarin dukiya ta al’umma da wadatar ƙasarmu, shakka babu shine yasa Najeriya ta zamo kan gaba a tsakanin bakaken fata a duniya sannan ta zamo abun alfahari da fatan Afrika, idan za mu iya haɗa kanmu tare don amfani da damarmu.

“Kasar da ke da mutum kusan miliyan 200 da doriya wadanda hazaƙarsu da begensu ke kyalkyali kamar lu’u lu’u mai daraja. “Yan Najeriya suna walƙiya kamar lu’u -lu’u a kebabbe, imma a fannin Ilimi, Kasuwanci, tunani, Kiɗa, Fim, Nishaɗi, Yanayi da al’adu. “Lallai mu ne kan gaba a baƙar fata a duk duniya kuma babu shakka alfahari da fatar Afirka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *