‘Yan bindiga sun kai hari kan sansanin sojojin Najeriya

‘Yan bindiga sun kai wani mummunan hari kan sansanin sojoji da ke Burkusuma a Karamar Hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto ta Najeriya, tare da hallaka mutane 15.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne da safiyar Juma’a a kauyen Dama da ke karamar hukumar Sabon Birnin.

Baya ga nan kuma maharan sun sake kai wani harin kauyen Katsira, inda nan kuma suka hallaka mutane hudu.

‘Yan bindigar sun zagaye sansanin, tare da fara bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya yi sandiyyar mutuwar mutane 15.

‘Yan ta’addar sun kuma kona motar sojoji guda biyu, tare da guduwa da guda daya, wadda suka yi amfani da ita wajen loda kayan abincin da suka sata daga wasu kauyuka.

Bayanai sun ce sojoji da dama sun bata, sakamakon harin, kuma tuni aka tura motoci cike da sojoji don bin bayan su a cikin dajin da suka tsere.

Wani jami’in hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence ya shaida wa manema labarai cewa cikin wadanda suka mutu har da jami’in hukumar guda uku.

Jami’an tsaro dai sun bukaci al’ummar yankin da su kwantar da hankulansu, tare da tabbatar musu da cewa sha’anin tsaro ya dawo yankin yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published.