Wanyama ya yi ritaya daga buga wa Kenya tamola

Fitaccen  dan wasan kwallon kafa na Kenya Victor Wanyama ya sanar da ritayarsa daga buga tamola, amma a matakin wasan kasa da kasa.

Wanyama wanda tsohon dan wasan tsakiya ne a Tottenham , ya ce, daukar wannan mataki na rataye takalmansa na da matukar wahala, amma ya zama dole.

Wanyama mai shekaru 30, wanda ya rike kaften din tawagar Kenya, ya ce, lokaci ya yi da ya kamata ya kauce domin bai wa ‘yan baya dama.

Ya shafe tsawon shekaru 14 yana buga wa Kenya tamola, yayin da ya kafa tarihin zama dan Kenya na farko da ya fara zura kwallo a gasar zakarun Turai, lokacin da kungiyarsa da Celtic ta doke Barcelona da ci 2-1 a kakar 2012.

Yanzu haka yana taka leda a CF Montreal ta Canada.

Leave a Reply

Your email address will not be published.