Rundunar yan sanda reshen jihar Oyo, ta gurfanar da wani matashi ɗan kimanin shekar 25 a duniya, Solomon Ochadi, a gaban kotun majistire dake zamanta a Ibadan, bisa zarginsa da hallaka mahaifiyarsa, Elizabeth Ochadi.
Punch ta rahoto cewa rundunar yan sandan ta gurafanar da manomin matashin ne kan zargi ɗaya tal, na kisan kai.
Karamin sufetan yan sanda, mai gabatar da ƙara, Opeyemi Olagunju, ya faɗa wa kotun cewa wanda ake zargin ya ingiza mahaifiyar tasa ne cikin rijiya.
Yace hakan ya yi sanadiyyar mutuwar matar yar kimanin shekara 50, wacce take uwa a gare shi, a cikin rijiya.
Da yake labartawa kotu yadda lamarin ya faru, mai gabatar da ƙara na rundunar yan sanda yace wanda ake zargin ya nemi abincinsa daga mahaifiyar tasa bayan ya dawo daga gona.
Yace:
“Matar ta shaida masa cewa babu abinci a gidan. Ba zato sai ya ingizata cikin rijiya saboda fushi da amsar da ta ba shi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.”
Olagunju, ya cigaba da shaidawa kotu cewa bayan ya kashe ta, Solomon ya nemi wuri a bayan gidansu ya yi wa gawarta ƙabari.
Kannen matashin, da suka ganewa idonsu abinda ya faru, sune suka sanar da yan sanda, kuma aka cafke wanda ake zargin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.