NATO na kokarin hana China fadada karfinta na nukiliya

Kungiyar Tsaro ta NATO ta bukaci China ta shiga cikin tattaunawar kayyade yawan makaman da kowacce kasa za ta iya mallaka a wani kokari na dakile yunkurin kasar na fadada sashenta na nukiliya.

Babban Sakataren Kungiyar ta NATO Jens Stoltenberg ya bayyana damuwa da yadda China ke ci gaba da fadada sashenta na nukiliya, yana mai cewa akwai bukatar kasar ta mutunta dokokin duniya wajen shiga tattaunawar kayyade yawan makaman don kauce hadarin da matakin nata ka iya haifarwa.

A cewar Stoltenberg yayin ganawarsa da Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi ta bidiyo, duk da kasancewar China ba ta cikin mambobin NATO amma yana da kyau ta mutunta dokokin kasa da kasa.

A zantawar tasu Stoltenberg ya ce akwai bukatar China ta rika bayyana wa duniya irin makaman da ta ke mallaka ba tare da nuku-nuku ba. Kazalika ya kamata ace ayyukanta na soji a fili sabanin yadda ta ke boyewa.

China dai na cikin jerin kasashen da ke da karfin makamin nukiliya a duniya, sai dai NATO na nuna fargaba a lokuta da dama dangane da rashin fayyace wa duniya matakin da ta kai a bangarenta na nukiliya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *