Jami’an ‘Yan Sanda sun cafko mutane 10 da suka kashe Matafiya a hanyar Filato

Rundunar ‘yan sanda na jihar Filato, sun gurfanar da wasu mutane 10 da ake zargin su da hannu a kashe wasu Fulani da ta tafiya ta bi da su ta Jos.

Jaridar Daily Trust tace an hallaka wadannan mutane ne yayin da suka bi ta titin Gada-biyu zuwa Rukuba, garin Jos, a jihar Filato a cikin tsakiyar watan Agusta.

Jami’an tsaron sun gurfanar da wadanda ake zargi da wannan laifi a babban kotun jiha da ke Filato.

Lauyar da ta tsaya wa ‘yan sanda, Muleng Alex, tace wadannan mutane 10 sun kashe wasu matafiya da suke kan hanyarsu ta zuwa Ondo, daga garin Bauchi.

Wadanda aka gurfanar a kotu sune Mathew Daniel, Juarbe Zamani, Dapar Sunday, Bernard Francis, Daniel Bulus, Solomon Dung, da kuma wani Yakubu John.

Ragowar wadanda ake zargi sun hada da; Stephen Ishaku, Yohanna Marshal, da Dakwak Sunday.

Muleng Alex tace wadanda ake tuhuma a gaban kotu sun auka wa matafiyan da miyagun makamai, tace Solomon Dung yaro ne da bai cika shekara 18 ba.

Lauyar ta roki Alkali ya tsare Dung a sashen taske kananan yara a gidan gyaran hali na Jos. Alex tace hukuncin wanda ya aikata wannan laifin shi ne kisan-kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *