EU ta raba wa mambobinta kudin tallafin Brexit

Gwamnatocin kasashen Turai sun amince da Euro biliyan 5 da miliyan 400 a matsayin kudaden tallafin gaggawa ga mambobin kasashen Turai da ficewar Birtaniya daga EU ta wujijjiga tattalin arzikinsu.

Daga karshe dai, gwamnatocin kasashen na Turai sun amince da lale makudaden kudaden tallafin, inda za a mika  kaso mafi tsoka ga Ireland da Faransa.

Ireland wadda ita ce kasa daya tilo da ta raba iyakar kan tudu da Birtaniya a Turai, za ta amshi Euro  biliyan 1 da miliyan 100 daga kudin domin gyagijewa daga koma-bayan tattalin arzikin da ta fuskanta saboda raba gari da Birtaniya.

Ita kuwa Faransa za ta samu Euro miliyan 735, inda za a zuba kaso mafi girma ga bangaren harkar Su, lura da cewa, wannan bangaren ya samu tawaya sakamakon karancin damar shiga cikin Kogin Birtaniya a yanzu.

A ranar 24 ga watan Disambar bara ne, gwamnatin Birtaniya da mahukuntan Brussels suka cimma matsaya cikin kurarren lokaci kan yarjejeniyar kasuwanci tsakanin bangarorin biyu bayan sun raba gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published.