Barcelona da Madrid da Juventus sun tsallake shari’ar UEFA

Hukumar Kwallon Kafa ta Turai UEFA ta janye karar da ta shigar kan kungiyoyin Real Madrid da Barcelona da Juventus a Kotu da suka amince da sabuwar gasar Super League ta Turai.

Kungiyoyin na kan gaba daga cikin jerin kungiyoyi 12 da suka yi kokarin kafa sabuwar gasar, wadda daga bisani ta wargaje bayan sauran kungiyoyin sun janye daya bayan daya.

Sai dai Real Madrid da Barcelona Juventus sun ki janyewa daga wannan gasa, abin da ya sa UEFA ta dauki matakin shari’a a kansu.

Sai dai UEFA din ta ce, daga yanzu tamkar ma babu wannan batu na tuhumar manyan kungiyoyin.

Wannan kuwa na zuwa ne bayan wata kotu a brinin Madrid ta hana UEFA hukunta kungiyoyin uku da suka ki janyewa daga gasar.

Amma har yanzu UEFA na kan bakarta ta rashin amincewa da sabuwar gasar ta Super League.

Leave a Reply

Your email address will not be published.