Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya ta jaddada cewa, ba dole ne mulkin kasar ya koma kudancin kasar saboda wannan tsarin ba ya cikin kundin mulki.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kudu ke ci gaba da tayar da kayar-baya domin ganin sun karbe ragamar shugabancin kasar a zaben 2023 mai tafe.