An karrama Buratai da lambr yabo a Lagos

An karrama tsohon babban hafson sojin kasa a Najeriya kuma jakadan kasar a Jamhuriyar Benin, Laftanar Yusuf Tukur Buratai da lambar yabo don jinjina masa kan rawar da ya taka a rayuwarsa ta aiki.

Mujallar Global Excellence ce ta karrama Buratai a wani gagarumin biki da aka gudanar a birnin Lagos da ke kudancin kasar a karshen makon da ya gabata.

Mawallafin Mujalar  Mayor Akinpelu ya ce, sun zabi Buratai ne don karrama shi saboda tarin gudun-mawar da ya bayar ta fuskar inganta tsaro da bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Koda yake Buratai wanda yanzu ke can Jamhuriyar Benin bai samu damar halartar bikin ba, amma Laftanar Janar Lamidi  Adeosun mai ritaya ne ya wakilce shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *