‘Yan bindiga sun saki karin daliban Bethel Baptist 10

‘Yan bindiga sun saki karin dalibai 10 na makarantar bethel Baptist da suka sace a Kaduna.

Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar ta Kaduna Joseph Hayab, ya ce an saki daliban ne da yammacin ranar Lahadi, kuma tuni an sada su da iyayensu.

A watan Yulin da ya gabata ‘yan bindiga suka yi awon gaba da dalibai 121, wadanda daga bisani suka rika sakin adadin yaran rukuni rukuni.

An dai sace daliban ne dai tun a ranar 5 ga watan na Yuli lokacin da gungun ‘yan bindigar suka kaiwa makarantar Bethel Baptist farmaki a karamar hukumar Chikun da ke Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published.