Sudan ta dakile yunkurin sojojin Habasha na yi mata kutse

Rundunar sojin Sudan ta sanar da dakile yunkurin kutsen da sojojin Habasha suka yi mata a yankin al-Fashaqa da ke kan iyakar kasashen biyu.

Sanarwar da rundunar sojin sudan ta fitar dai ba ta yi karin bayan ikan arrangamar da dakarun nata suka yi da na kasar ta Habasha ba, illa kawai cewar da ta yi an dakile yunkurinsu na yin kutse daga yankin Umm Barakit a ranar Lahadi.

Kawo yanzu dai kakakin rundunar sojin Habasha Kanal Getnet Adane, bai amsa tambayar da aka yi masa dangane da lamarin ba.

Tashin hankali a kan iyakar Sudan da Habasha ya karu ne tun bayan barkewar rikici a yankin Tigray na arewacin Habasha a shekarar bara wanda ya tagayyara dubban mutane da a yanzu ke gudun hijira a gabashin Sudan.

Rikicin na baya bayan nan tsakanin dakarun na Sudan da na Habasha ya auku ne a wani yankin al-Fashaqa mai albarkar kasar gona inda suka shafe shekaru suna takaddama akai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *