Sojin Najeriya sun cafke kasurgumin shugaban ‘yan bindiga mai suna Goma Sama’ila

Rundunar Sojin Najeriya ta samu nasarar cafke shugaban ‘yan bindiga da barayin shanu, Alhaji Goma Sama’ila.

An tattaro daga jaridar SaharaReporters cewa, an damke Samaila ne a jihar Kaduna da yammacin Juma’a 24 ga watan Satumba.

Rahotannin shaidun gani da ido sun nuna cewa Sama’ila ne ke da alhakin shirya satar shanu da dama a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.

An ce yana cikin wasu ayyunkan barna na garkuwa da mutane da dama a fadin jihohin.

Jihar Kaduna tana ci gaba da shan fama da barnar masu garkuwa da mutane, kisan gilla da satar shanu daga ‘yan bindiga.

Wata majiya ta ce:

“Sojojin Najeriya sun cafke Goma Sama’ila, daya daga cikin “ wadanda ake nema” kuma kasurguman shugabannin ‘yan bindiga da ke addabar Zamfara, Kaduna, Katsina da sauran jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Wannan ci gaba na zuwa ne yayin da sojoji ke aikin kakkabe ‘yan ta’adda a yankin.

A baya mun kawo muku rahoton cewa, an kashe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara don shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi jihar.

Jihar Katsina, duk da kasancewar mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta sha fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayuka da dama.

Fiye da mutane 700 ne ‘yan bindiga suka kashe a kananan hukumomin Jibia, Kankara, Dutsinma, Musawa, Danmusa da Safana na jihar a cikin watanni biyar da suka gabata.

Gwamnatin jihar Sakkwato ta kuma katse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 cikin 23 na jihar a wani bangare na kokarin kakkabe ‘yan ta’adda a dazukan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *