Mutane 67 sun mutu a sabon rikicin Yemen

Akalla ‘yan tawaye da sojojin gwamnati 67 ne suka rasa rayukan su a rikicin da ke cigaba da faruwa a birnin Marib na kasarYemen.

Kasar Saudiya ce ta jagoranci hare-haren da aka kai wa ‘yan tawayen Huthi, da ke shirin kwace birnin Marib mai arzikin man fetur.

Daruruwan mayaka ne suka rasa rayukansu a rikicin Marib na wannan watan, wanda hakan ya tilasta wa dubban mazauna yankin yin hijira.

Sojojin yankin, sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, mayakan Huthi 58 da soji 9 ne suka rasa rayukansu a rikicin da ya auku a cikin sa’o’i 24 da suka gabata a Marib da kuma Shabwa.

A cewar wata majiyar soji da ta nemi a sakaya sunanta, a cikin wadannan sa’o’i 24 kawai, jiragen yakin Saudiya sun yi barin wuta akalla sau 20 a kan ‘yan tawayen Huthi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *