Messi ya samu lafiyar karawa da Manchester City

Akwai yiwuwar Lionel Messi ya kasance cikin tawagar PSG da za ta fafata da Manchester City a gasar cin kofin zakarun Turai a gobe Talata bayan murmurewarsa daga raunin da ya samu a guiwarsa.

Messi wanda ya taba doka tamola karkashin jagorancin kocin Manchester City na yanzu Pep Guardiola, har yanzu bai zura kwallo a raga ba a cikin wasanni uku da ya buga wa  sabuwar kungiyarsa ta PSG.

Dan wasan ya rasa damar buga wasanni biyu na baya-bayan da PSG ta yi saboda wannan rauni a guiwarsa.

Kocin PSG, Mauricio Pochettino ya ce, Messi na cikin karsashi a yanzu kuma akwai yiwuwar ya kasance cikin tawagar da za ta yi wasan gobe a gasar zakarun Turai a cewarsa.

Koda yake Pochettino ya ce, kawo yanzu bai yanke shawara ba  dangane da tawagar farko da za ta yi masa wasan.

Babu shakka fafatawar ta gobe za ta ja hankali domin kuwa PSG din na fatan rama abin da City ta yi mata a kakar da ta gabata, inda ta doke ta da jumullar kwallaye 4-1 a matakin wasan gab da na karshe a gasar ta zakarun Turai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *