Masu laifi na dakon hukuncin rajamu a Bauchi

A jihar Bauchin Najeriya, sama da shekaru 20 kenan  da kaddamar da  tsarin shari’ar Musulunci, amma har yanzu ana fuskantar jinkiri wajen aiwatar da hukunce-hukuncen da kotuna suka yanke karkashin wannan dokar.  Ya zuwa wannan lokacin dai, wadanda aka yanke wa hukuncin rajamu ko yanke-hannu karkashin dokar ta Islama, na can na jiran tsammani a gidajen kurkuru duk tsawon wadanan shekaru. 

Tun shekara ta 2001 da jihar Bauchi ta shiga sahun jihohin arewacin Najeriya da ke amfani da tsarin shari’ar musulunci, aka fara fuskantar tsaiko wajen aiwatar da hukunce-hukuncen da aka yanke karkashin wannan dokar.

Wadanda kotunan na shari’ar musulunci suka yanke wa hukuncin yanke-hannu ko rajamu,na can na jiran tsammani watau ta fannin daukaka kara ko aiwatar da wannan hukuncina  kansu.

Wannan yanayi da aka shiga ya jefa Hukumar Aiwatar da Shari’ar a jihar Bauchi cikin tsaka-mai-wuya kamar yadda Mallam Mustapha Baba Illela, shugaban Aiwatar da Shari’ar Musulunci a jihar Bauchin ya shaida wa RFI Hausa, inda ya ce,

Mu Hukumar Shari’ar Musulunci muna da iyaka. Na farko dai mu fadakar kada a yi sabo wato ta fannin shan giya ko zina…in kuma har an kama mutum da laifin aikata wannan to sai mu mika shi ga alkali domin tabbatar da laifinsa…..in mun yi haka to aikinmu ya kare….sauran aiwatarwar yana da matakai daban-daban.

A halin da ake ciki dai yanzu Hukumar Kula da Gidajen Kaso ta kasa reshen jihar ta Bauchi wato wadanda ke daiwainiya da wadanda aka yanke wa hukuncin yanke-hannu ko rajamu na tsawon wadannan shekaru, ta gabatar da kuka gaban babban joji na jihar domin samun mafita kan makomar wadannan rukunin mutanen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *