Mai yiwuwa a dage zaben Mali da zai gudana a 2022 – Firaminista

Firaministan Mali Choguel Kokalla Maiga, ya ce mai yiwuwa a dage zaben kasar da aka shirya yi a farkon shekara mai zuwa.

Maiga ya bayyana haka ne yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na AFP a yau Lahadi, inda ya kara da cewa yanzu haka gwamnatin Mali na kulla yarjejeniyar inganta tsaro daga wasu abokan hulda daga kasashen ketare, a daidai lokacin da Faransa ke shirin rage yawan sojojinta a kasar da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda.

Firaministan na Mali ya ce za a iya dage zabukan kasar na watan fabarairu ne da akalla watanni 2,  idan har aka cimma matsaya kan kudurin yayin taron da za su yi a watan Oktoba.

A cewar Maiga yana da kyau a shirya zabuka cikin lumana, da kowa zai amince sakamakonsa a maimakon shirya zabukan da zai haifar da rikici.

Shugaban gwamnatin sojin kasar Mali Kanal Assimi Goita, a birnin Bamako. © REUTERS – AMADOU KEITA

Zaben, da shugaban rikon kwaryar gwamnatin sojin Mali mai hadaka da farar hula Kanal Assimi Goita ya yi alkawarinsa a watan Fabrairu na shekarar 2022, na da nufin maida mulki ga farar hula bayan juyin mulkin da ya jagoranta yi a watan Agustan bara na kawar da tsohon shugaban Ibrahim Boubacar Keita.

A waccan lokacin ne dai, sojojin suka nada gwamnatin farar hula ta wucin gadi da aka dorawa alhakin mayar da mulkin dimokradiyya, amma Goita ya sake yin juyin mulki karo na biyu a watan Mayu tare da ayyana kansa a matsayin shugaban kasa.

Duk da cewa Kanal Goita ya yi alkawarin mutunta wa’adin zaben na watan Fabrairu tare da sanya ranar 31 ga watan Oktoba a matsayin ranar gudanar da zaben raba gardama kan kundin tsarin mulki.

Amma a farkon wannan watan na Satumba, kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta ce tana fargabar yiwuwar samun jinkirin gudanar da zaben sabuwar gwamnati a kasar ta Mali.

Leave a Reply

Your email address will not be published.