Joshua bai daddara da dukan da ya sha a hannun Usyk ba

Fitaccen dan damben boxing na Ingila dan asalin Najeriya, Anthony Joshua ya kafe kan cewa zai iya fafatawa da Tyson Fury wani fitaccen dan damben na boxing wani lokaci nan gaba kadan, koda kuwa ba tare da kambunansa guda uku na duniya ba.

A ranar Asabar din da ta gabata, Joshua ya rasa kambunsa na zakaran damben boxing na duniya ajin masu nauyi da suka hada da WBA, IBF da kuma WBO, bayan kayen da ya sha a fafatawar da yayi da Oleksandr Usyk a filin wasa na kungiyar Tottenham Hotspur.

Sai dai tuni wakilan Anthony Joshua suka tabbatar da cewa zai sake fafatawa da Usyk domin kwato kambunsa guda 3, yayin da shi kuma Joshua ke jin har yanzu yana karawa da Tyson Fury ko da ba tare da lambobinsa na duniya ba.

Rashin nasarar da Joshua ya yi a karon battarsa da Oleksandr Usyk a ranar Asabar, itace karo na biyu da fitaccen dan damben boxing din ya fuskanta tun bayan ficen da yayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *