Gwamnatin Sudan ta sasanta da masu zanga-zanga

Gwamnatin Sudan ta cimma matsaya da jagororin masu zanga-zanga domin bude hanyar shigar da danyen man fetur cikin kasar ba tare da shamaki ba daga Sudan ta Kudu.

Gwamnatin Sudan na samun kudaden shiga daga man fetur din da ake shigo da shi daga makwabciyarta Sudan ta Kudu, inda akan kowacce ganga guda take karbar Dala 25, kudin da ke taimaka mata wajen bunkasa tattalin arzikinta.

Sudan ta Kudu dai na fitar da akalla ganguna dubu 162 a kowacce rana na man fetur wadanda ake shigar da su cikin Sudan ta bututu kafin daga bisani a fitar da su zuwa kasuwannin duniya.

Sai dai a ‘kwanakin  nan, masu zanga-zanga sun datse tashar jiragen ruwa ta Bashayer domin hana safarar man fetur din daga Sudan ta Kudu, amma a yanzu an sasanta  tsakanin masu boren da bangaren gwamnati.

Tun a farkon makon jiya ne masu zanga-zangar ‘yan kabilar Beja suka toshe hanyoyin safarar man fetur din a wani mataki na nuna rashin amincewa da wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin gwamnatin Sudan da wasu kungiyoyin ‘yan tawayen kasar, baya ga kokawar da suke yi kan abin da suka kira rashin adalcin da suke gani a yankinsu da ke gabashin Sudan.

Masu zanga-zangar sun ce, wannan yarjejeniyar da aka cimma da ‘yan tawayen Darfur da Blue Nile da Kudancin Kordofan ta saba da muradunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.