Arsenal ta zazzagawa Tottenham kwallaye uku cikin mintuna 35

Arsenal ta zazzagawa kungiyar Tottenham kwallaye uku cikin mintuna 35 a wasan gasar firimiyar da suka fafata jiya Lahadi, wanda daga karshe Arsenal din ta samu nasara da kwallaye 3-1.

‘Yan wasan Arsenal Emile Smith Rowe, Aubameyang da kuma Bukayo Saka ne suka ci kwallayen 3, yayin da Song Heung-min ya ci wa Tottenham guda.

A makwanni uku da suka gabata dai, Tottenham na cikin kungiyoyin da ake saman teburin gasar Firimiyar Ingila, yayin da Arsenal ke zaman ta karshe ba tare da maki ko daya ba, bayan lallasan da aka sau uku jere da juna, a wasannin da ta fafata da Brentford, Chelsea da kuma Manchester City, mafi munin farkon kakar wasa da kungiyar ta Gunners ta gani cikin shekaru 67.

Sai dai a halin yanzu Arsenal din ta farfado bayan lashe. wasanni uku a jere da suka hada da wanda ta doke, Norwich, da Burnley dukkaninsu da 1-0, sai kuma jiya da ta lallasa Tottenham da 3-1 abinda ya sa a yanzu ta koma ta 10 da maki 9.

A sauran wasannin karshen makon da aka buga a gasar Firmiyar ta Ingila dai, Manchester City ta doke Chelsea ta 1-0, abin da ya kawo karshen rashin shan kayen kungiyar ta Chelsea ta yi tun bayan fara kakar wasa ta bana.

Liverpool da Brentford sun tashi 3-3, yayin da Manchester United ta yi rashin nasara a fafatawar ta da Aston Villa da 1-0.

A wasu daga cikin wasannin La Liga a Spain kuwa, Sevilla ta doke Espanyol da 2-0, Real Madrid kuwa da kyar ta shay ayin karawa da Villareal inda suka tashi 0-0, yayin da Barcelona ta lallasa Levente da 3-0.

A gasar Ligue 1 ta Faransa PSG da har yanzu Lionel Messi bai samu ci mata kwallo ba, ta samu nasara kan Montpellier da 2-0.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *