An gano matsugunin gidan rediyon Nnamdi Kanu da ke tunzura tsageru

Shekaru da yawa kenan ‘yan Najeriya ke neman sanin inda ‘Radio Biafra’, cibiyar rediyon kafar intanet wanda ke watsa ajandar ‘yan haramtacciyar kungiyar IPOB take.

Jiya, gidan talabijin na CNN, ya gano wani titi mai cike da ganye a Peckham, kudu maso gabashin London, adireshin kungiyar ta IPOB kenan, Vanguard ta ruwaito.

Gidan talabijin na CNN ya bayyana wurin a matsayin wurin da ke kusa da birni, yana mai cewa wannan wuri ne da ba a zata ba ga gidan Rediyon Biafra.

Mazi Nnamdi Kanu ya kafa haramtacciyar kungiyar IPOB a 2012 inda kuma ya kafa Rediyon Biafra a 2009. An kirkiro kungiyar ne domin maido da fafutukar kafa kasar Biafra mai cin gashin kanta.

An kuma kirkiro ‘Radio Biafra’ don yadawa, fadakarwa, ilimantarwa, sanarwa da sukar ayyukan gwamnatin Najeriya da Kanu ke yi. Gwamnatin Tarayya ta haramta kungiyar IPOB a shekarar 2017.

Amma kafin nan, a ranar 19 ga watan Oktoba, 2015, an kama Kanu da laifin cin amanar kasa, tayar da zaune tsaye, da tayar da fadan kabilanci. An sake shi bisa beli a 2017 kuma ya gudu zuwa Burtaniya.

Kungiyar IPOB ta soki gwamnatin tarayyar Najeriya kan rashin saka hannun jari mai kyau, nisantar siyasa, rabon albarkatun kasa, nuna wariya, yawan sojoji, kashe-kashe a yankin Kudu maso Gabas, Kudu maso Tsakiya da sassan yankunan Arewa ta Tsakiya na kasar.

An sake kama Kanu a baya-bayan nan a kasar Keyan inda aka kunso shi zuwa Najeriya don fuskantar tuhumar da ake masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.