Sojin Najeriya sun dakile farmakin da ISWAP suka kai sansanin soji da wasu yankunan Yobe

A yammacin ranar Alhamis ne dakarun sojin Najeriya su ka yi nasarar dakile wani farmaki da ‘yan ta’addan Islamic State of West Africa Province (ISWAP) suka kai sansanin soji da kuma wasu yankuna na jihohin Borno da Yobe.

PRNigeria ta gano cewa, dakarun dauke da manyan makamai sun bankado yunkurin harin da miyagun ‘yan ta’addan suka kai Malam Fatori da ke jihar Borno.

‘Yan ta’addan da suka bayyana a motocin yaki da babura, zakakuran dakarun sun fi karfinsu inda suka batar da wasu daga ciki yayin da wasu suka ja da baya tare da tserewa.

Har ila yau, kusan a lokaci daya, dakarun sojin da ke jihar Yobe sun dakile wani farmakin da ISWAP ta kai yankin Babangida.

Wata majiyar tsaro ta sanar da PRNigeria cewa dakarun sun fatattaki ‘yan ta’addan har zuwa wurin kauyen Jalingol da ke kusa da yankin Jauro a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *