Jerin shugabannin Afirka mafi tsufa da ke kan mulki, an bayyana matsayin Buhari

A Afirka gaba ɗaya, furfura alama ce ta hikima da gogewa, wanda shine dalilin da ya sa yawancin shugabanni a nahiyar suka kasance tsofaffi wadanda cikinsu akwai ƙwararrun masana.

An tattara tare da lissafa jerin shugabannin Afirka na yanzu da suka tsufa a wannan wallafar.

1. Paul Biya (shekaru 88)

Mutum na farko a jerin shine shugaban kasar Kamaru, Paul Biya. An haifi Biya a ranar ga watan Fabrairu 1933 a Mvomeka’a, Ntem, Kamaru na Faransa. A yanzu yana da shekaru 88 kuma shine mafi tsufa a cikin shugabannin bakar fata.

2. Hage Geingob (shekaru 80)

An haifi shugaban Namibia, Hage Geingob a watan Agustan 1941.

3. Evaristo Carvalho (shekaru 80)

Ko da yake shekarunsu ɗaya da Geingob (1941), shugaban Sao Tome and Principle, Evaristo Carvalho ya zo a baya saboda an haife shi a watan Oktoba.

4. Alassane Ouattara (shekaru 79)

Shugaba Ouattara na Ivory Coast wanda ke kan mulki tun 2010 an haife shi a ranar 1 ga watan Janairun 1942 a Dimboko.

5. Teodoro Nguema Mbasogo (79)

Na gaba shine Teodoro Nguema Mbasogo na Equatorial Guinea. An haifi tsohon hafsan sojan a ranar 5 ga watan Yunin 1942 a Acocan, Equatorial Guinea.

6. Muhammadu Buhari (shekaru 78)

An haifi shugaban Najeriya na yanzu a ranar 17 ga Disamba a Daura, jihar Katsina. Yana kan kujerar mulki a karo na biyu bayan ya yi shugabanci a lokacin mulkin soja tsakanin 1984 zuwa 1985.

7. Nana Akufo-Addo (shekara 77) Na bakwai shine shugaban kasar Ghana. Nana ya kasance shugaban kasa tun 2017. An haife shi a ranar 29 ga Maris 1944 a Accra, babban birnin kasar.

8. Yoweri Museveni (shekaru 77) An haife shi a ranar 15 ga Satumba 1944 a Ntungamo, shugaban na Uganda shine na takwas a wannan jerin. Kafin ya kai ga zama shugaban kasa, Museveni babban jami’in soji ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *