Gwamnan jihar Kaduna ya nada Sarki Muhammasu Sanusi matsayin Uban jami’ar KASU

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya nada Sarkin Kano an 14, Muhammadu Sanusi na biyu, a matsayin sabon Cansalan Jami’ar jihar Kaduna KASU.

An nada tsohon Sarkin Kanon ne a taron yaye daliban jami’ar da akayi a ranar Asabar, 25 ga Satumba, 2021 a jihar Kaduna.

Gwamnan da kansa ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Facebook. El-Rufa’i ya bayyana farin cikinsa na nada Sarki Sunusi wannan mukami.

Yace:

“An nada Mai Martaba Muhammadu Sanusi II matsayin Cansalan jami’ar jihar Kaduna (KASU), bayan haka kuma ya jagoranci taron yaye dalibai na hudu a jami’ar.”

“Ina matukar farin cikin nada Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II matsain Uban jami’ar Kaduna.” “Gwamnatin jihar Kaduna na farin ciki Muhammadu Sanusi II ya karbi wannan sabuwar nadi da mukayi masa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *