Firaministan Mali ya soki matakin faransa na ficewa daga Mali

Firaministan Mali Choguel  kokalla Maiga yayinda da yke gabatar da jawabi a zauren majalkisar Dinkin Duniya ya zargi Faransa da taka muguwar rawa a wannan lokaci da Mali da aminan ta ke ta kokarin ganin sun kawo karshen rashin tsaro dama dawowwa turbar Demokuradiyya.

Faransa a cewar sa  ta kama hanyar janye dakarun ta na rundunar Barkhane,yan lokuta bayan da Rasha ta hanyar daya daga cikin kamfanin Tsaro na Wagner mai zaman kan sa ya amince ya kawo ta sa gundumuwa a batun tsaro da ya shafi arewacin kasar ga baki daya.

Firaministan Mali ,da babbar murya ya na mai cewa ,cewa Faransa ta janye dakarun ta a wannan lokaci tamkar cin amanar Mali ne ,hakan zai baiwa kasar ta Mali zabi don ganin ta tabbatar da kuma kare kasar ga baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.