Faransa ta gargadi Rasha kan katsalandan a rikicin Mali

Ministan harkokin wajen Faransa ya gargadi takwaransa na Rasha game da shigar da sojojin hayar kasar sa daga kamfanin Wagner cikin rikicin kasar Mali, matakin da ya ce zai maida kasar ta Mali saniyar ware a duniya.

Kafin gargadin na Jean-Yve Le Drian a ranar Juma’a sai da ministan harkokin wajen na Faransa ya gana da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov a ranar Alhamis, yayin gudanar taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, gwamnatin sojin Mali na gaf da daukar sojojin haya dubu 1 daga kamfanin Wagner na Rasha domin taimaka mata wajen tabbatar da tsaro.

Kasashen yammacin Turai sun dade suna zargin cewa kamfanin Wagner mai alaka ta kusa da shugaban Rasha Vladimir Putin da yin aiki a madadin gwamnatinsa.

Sojojin haya daga kasar Rasha daga kamfanoni masu zaman kansu, sun kara yin tasiri a Afirka cikin ‘yan shekarun nan, musamman a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai fama da rikici, inda Majalisar Dinkin Duniya ta zargi’ sojojin Wagner da aikata laifukan cin zarafin dan Adam.

Leave a Reply

Your email address will not be published.