Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen G20 da su fadada shirin su na dakatar da karbar biyan basussuka zuwa ga dukkanin kasashe matalauta.
Buhari ya yi wannan kira ne a lokacin da yake yi wa shugabannin duniya jawabi a wurin Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76 a birnin New York na Amurka a jiya Juma’a.
Shugaban ya kuma yi kira ga kasashen masu arziki da su soke baki dayan bashin da suke bin kasashen da ke fuskantar tasiri mafi muni da annobar Korona ta haifar.
A bangaren tsaro kuwa, shugaban Najeriyar ya bukaci taron majalisar dinkin duniyar ya karfafa aiwatar da yarjejeniyar cinikin makamai ta duniya, a dukkanin kasashe don daidaita shige da ficen makamai, matakin da ke da mahimmanci ga tsaron kasashe.
Buhari ya kuma yi gargadin cewa yawaitar yaduwar kananan makamai a sassan duniya na barazana ga ayyukan jin kai da zamantakewa, musamman a nahiyar Afirka.