Babbar jami’ar kasar Birtaniya dake aiki a Najeriya, jiya asabar ta bayyana cewa kasar ta daga ranar 4 ga watan Oktoba za ta kawo sassauci dangane da matakan da ta dau da suka shafi yaki da cutar Covid 19 ga matafiya zuwa Birtaniya.
Catriona Laing ta ce ba za a sake fuskantar wata matsalla da ta shafi allurar da ake yiwa jama’a a Najeriya da zaran suke da niyar zuwa Birtaniya.

Jami’ar ta ce Birtaniya ta amince da alluran Oxford Astra Zeneca,Moderna,Pfizer da Johnson& Johnson da ake yiwa jama daga Najeriya.

Kasar ta Birtaniya ta taimakawa Najeriya da allurai kusan milyan daya da dubu dari biyu a shiri na Covax ,kuma za ta ci gaba da kawo na ta gundumuwa zuwa Najeriya na gaba.