An gano wasu mutane dake dauke da kwayar cutar covid 19 a Najeriya

Hukumomin yaki da cuttuka a Najeriya sun bayyana mutuwar mutane uku sanadiyyar cutar Covid 19,yayinda hukumar ta bayyana cewa an gano wasu mutane 477 da suka kamu da kwayar cutar cikin dan kankanin lokaci a jihohin kasar 17 da babban birnin tarraya Abuja.

Wanan kididiga ta fito ne daga hukumar yaki da cuttuka ta kasa NCDC a marecen juma’a.Ga baki daya hukumar ta fitar da alkaluma dake dada nuni cewa ga baki daya tun bayan bulluwar cutar a Najeriya akalla mutane dubu 203.991 ne suka harbu da kwayar cutar inda aka samu mutuwar mutane 2.671.

Ya zuwa yanzu kam ,jihohin kasar hudu da suka hada da Nasarawa,Ondo ,Osun da Sakoto ne suka cira daga cikin yankunan da babu wanda ya kamu da kwayar cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *