An gano wasu mutane dake dauke da kwayar cutar covid 19 a Najeriya

Mai dakin Shugaban kasar Brazil Michelle Bolsonaro da aka yiwa allurar rigakafin cutar Covid 19  a New York daf da soma babban taron kasahen Duniya na Majlisar Dinkin Duniya na ci gaba da shan suka, kungiyoyi na kalon ta a matsayi wacce ke kokarin kawo cikas ga wannan tafiya musaman na yiwa al’uma wannan allura  kasancewarta  matar shugaban kasa wacce ta kaucewa yin wannan allura.

Sai dai Shugaban na Brzail ya yi kokarin kare matar sa inda yak e cewa yanzu haka bai karbi wannan allura ba,fatan sa shine na kasancewa dan kasar Brazil na karshe da za a yiwa wannan allura nan  gaba,sabili da haka ya yi watsi da kalaman wadanan kungiyoyi dake danganta matar sa da wacce ba ta muntunta ayyukan jami’an kiwon lafiya a wannan tafiya na yaki da cutar Covid 19.

Brazil na daga cikin kasashen da cutar Covid ke yiwa al’umarta barazana,inda alkaluma ke dada nuni cewa mutane da dama ne suka mutu bayan kamuwa da kwayar cutar tun bayan bulluwarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *