‘Yan bindiga sun aika wa al’ummar Shinkafi wasikar hari

‘Yan bindigar da ke shan ragargaza a hannun sojojin Najeriya sun aike da wata wasika ga al’ummar Shinkafi ta jihar Zamfara, inda suka sanar da shirinsu na kai musu farmaki.


Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa, ‘yan bindigar na dandana kudarsu a hannu sojojin Najeriya da aka tura su domin murkushe su.


Dr. Shinkafi ya kuma bayyana cewa, sun samu rahotannin da ke tabbatar cewa, ana nan ana harbe-harbe a halin yanzu a garin.


Tuni dai gwamnati ta katse hanyoyin sadarwar wayar salula domin bai wa sojojin damar gudanar da ayyukansu na luguden wuta kan ‘yan bindigar yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *