Rundunar Sojin Najeriya ta sha alwashin hana ISWAP cika kudirinta a kasar

Rundunar Sojin Najeriya ta yi ikirarin cewa za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen hana kungiyar ISWAP aiwatar da kudirinta na rusa kasar, bayan da ta ke ci gaba da karfafa hare-harenta musamman yankin arewa maso gabas.

Kwamandan rundunar Operation Hadin kai Manjo Janar Christopher Musa da ke bayyana kungiyar ta ISWAP a matsayin wadda ta shiga Najeriyar daga ketare bisa kudirin rusa kasar kuma ta ke samun goyon bayan tsirarun mayakan ta’addanci, ya ce dakarun rundunar Soji ba za su taba barinta ta ci gaba da ta’addanci a kasar ba.

A cewar Janar Musa yayin wata zantawarsa da manema labarai a birnin Maiduguri na jihar Borno, zai fi dacewa ga wadanda ke marawa kungiyar baya kama daga mayaka da kuma daidaikun jama’a, su sani cewa ISWAP ba ta da hadi ta kowacce fuska da Najeriya, kuma manufarta shi ne ruguza kasar.

Acewarsa ISWAP kungiya ce da wasu ke daukar nauyinta daga ketare don kaddamar da hare-hare a sassan Najeriya ta yadda za ta samu gurbin mamaya a kasar.

Ko a makon da ya gabata sai da kungiyar ta ISWAP ta kashe sojin Najeriya 18 baya ga jikkata wasu 11 baya ga yin garuwa da wasu Sojin 2, harin da yak e matsayin mafi muni da kungiyar ta kaddamar tun bayan rahoton kisan jagoranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *