Ronaldo ya zarta Messi wajen samun kudi

Mujallar Fobes ta rawaito cewa, Cristiano Ronaldo na Manchester United ya yi wa Lionel Messi na PSG fintikau, inda a yanzu ya dare duk wani dan wasan kwallon kafa a duniya wajen samun albashi mafi tsoka.


Ronaldo zai samu jumullar Dala miliyan 125 kafin fitar da kudaden haraji kenan a cikinn wannan kaka ta 2021-2022.
Dan wasan zai samu Dala miliyan 70 daga albashinsa da kuma kudaden alawus-alawus da Manchester United za ta ba shi.


Sauran kudaden za su fito ne daga kamfanonin da dan wasan ke yi musu tallace-tallace kamar Nike da Herbalife da sauransu.


Mujallar ta Forbes ta ce, Ronaldo na cikin sharaharrun ‘yan wasa a duniya, inda yake da mabiya fiye da miliyan 500 a shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram da kuma Twitter.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *