Najeriya ta manta da gwarzon da ya daga darajarta a kwallon kafa

Tsohon kocin tawagar mata ta Super Falcons ta Najeriya, Isma’ila Mabo ya bayyana cewa, Hukumar Kwallon Kafar kasar NFF ba ta yi masa wani tanadi ba domin halartar gagarumin bikin karrama tsoffin ‘yan matan na Super Falcons da aka gudanar a birnin Lagos a farkon wannan makon.

Mabo mai shekaru 77, wanda kuma ake kallon sa a matsayin kocin da ya fi samun nasarori a Najeriya, ya jagoranci Super Falcons zuwa matakin wasan gab da na kusan karshe a Gasar Cin Kofin Duniya ta mata a 1999.

Kazalika ya jagoranci wannan tawaga har zuwa matakin wasan dab da na kusan karshe a Gasar Motsa Jiki ta Olympics a 2004.

Rashin halartar kocin wannan gagarumin biki a Lagos a ranar Litinin da ta gabata, ya haifar da kace-nace a Najeriya, inda wasu ke ganin cewa, har yanzu ana fama da matsalar nan ta an ci moriyar ganga, an yada kwaurenta.

Koda yake Mabo ya ce, NFF ta yi kokarin tuntubar sa amma ta hanyar wata mamba a kwamitin da ya shirya bikin karramawar, amma duk da haka  babu wani tanadi da aka yi masa a cewarsa.

Kawai dai an sanar da shi cewa, za a gudanar da bikin ne kadai, amma babu wani karin bayani inji shi.

Daga cikin ‘yan matan da aka gayyato domin karrama su har da wadanda ke zaune a Amurka da wasu kasashen Turai, yayin da matan suka bayyana takaicinsu na rashin tozali da tsohon kocin nasu a wurin bikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *