Najeriya ta gano masu tallafa wa Boko Haram – Malami

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi nasarar gano tare da tsare wasu fitattun mutane da ake zargi da tallafa wa ayyukan ta’addanci a kasar kamar yadda Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana.


Malami ya bayyana haka ne a hirarsa da Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya NAN a birnin New York na Amurka.
Koda yake Malami ya ce, ba zai yi rika malam masallaci ba wajen zurfafawa a cikin bayanansa saboda a haklin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.


A cikin watan Mayun da ya gabata ne Malami ya ce, gwamnatin Najeriya na shirin fara tuhumar wasu mutane 400 cikinsu kuwa har da wasu fitattu da ake zargi da bai wa Boko Haram kudaden tallafi.


Sai dai an yi ta caccakar gwamnatin kan jinkirta tuhumar mutanen, amma Malami ya bada tabbacin cewa, gwamnatin tarayyar ta dukufa wajen daukar tsauraren matakan yaki da ta’addanci a kasar, yana mai bada da misali da irin nasarar da ake samu kan mayakan Boko Haram da kuma ‘yan bindiga da suka addabi kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *