Buhari ga shugabannin duniya: Mun nakasa Boko Haram, kananan wurare su ke kai farmaki yanzu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce an raba kan mayakan Boko Haram kuma an rusa su.


TheCable ta ruwaito cewa, a cewar sa, duk da kokarin sojoji wurin ragargazar su har yanzu suna ta’addancin su kuma ba su daina kai farmaki ba.


Ya yi wannan furucin ne a ranar Juma’a a wani taron majalisar dinkin duniya a birnin New York dake Amurka.
A cewar sa:


Ta’addanci na ci gaba da yaduwa a fadin duniya. A Najeriya, duk da sojoji sun raba kan kungiyar Boko Haram kuma an rusa ta, ta na ci gaba da kai wa jama’a farmaki. Najeriya za ta ci gaba da yin aiki tukuru da UN wurin ganin an kawo karshen ta’addanci a kasar.


“Najeriya ta yi iyakar kokarin ganin ta kawo karshen Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya da yankin tafkin Chadi, da kuma ‘yan bindiga da suke addabar arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.


“Jami’an tsaron Najeriya sun samu nasarori masu tarin yawa yayin yaki da ta’addanci. Sakamakon kaimin da sojoji suka kara, mayaka da dama sun zubar da makamansu.”


Shugaba Buhari ya ce gwamnatin sa za ta yi iyakar kokarin ganin ta samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga mata, yara, masu nakasa, ‘yan gudun hijira da sauran su.


Ya yi kira ga duniya a kan a taru a kawo karshen cin zarafin da ake yi wa mata da yara, TheCable ta wallafa.
Shugaban kasa ya kara da kira a kan tsanar da ke karuwa a fadin duniya na banbancin launin fata da sauran su tsakanin jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *