Anya Koeman zai kai labari kuwa a Barcelona?

Kocin Barcelona Ronald Koeman ya ci gaba da fuskantar matsin lamba bayan kungiyarsa ta yi canjaras babu ci tsakaninta da Cadiz a jiya a gasar La Liga ta Sifaniya.


Jan katin da aka manna wa Frenkie Jong ya tilasta wa Barcelona kammala wasan da jumullar ‘yan wasa 10, inda a dayan bangaren alkalin wasa ya kori shi kansa Koeman ana gab da tashin wasan sakamakon gardamar da ya yi kan hukuncin alkalin na bai wa Sergio Busquets katin gargadi.


Kocin ya yi korafi kan jan katin da alkalin ya ba shi, yana mai cewa, kasar Spain ne kawai ake irin wannan hukuncin babu gaira babu dalili a cewarsa.


Yanzu haka wasannin La Liga biyu kacal daga cikin biyar Barcelona ta samu nasara, lamarin da ya dada zafafa hasashe game da makomar Koeman.


Ba a dai sani ba ko Koeman zai ci gaba da jagorancin kungiyar kafin nan da ranar Lahadi mai zuwa, ranar da Barcelona za ta yi wasanta na gaba da Levante a gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *