Al’ummar Mali na zanga-zangar goyon baya ga shirin dakko Sojin hayar Rasha

Daruruwan mutane ne suka shiga wata zanga zanga a Bamako babban birnin kasar Mali domin bayyana goyan bayan su akan shirin gwamnatin Sojin kasar na dauko sojojin haya daga Rasha domin yaki da Yan ta’adda.

Zanga zangar ta biyo bayan ziyarar da ministar tsaron Faransa Florence Parly ta kai Mali inda ta gargadi shugabannin kasar cewar kulla yarjejeniya da Rasha zai sa Faransa da Turai da Majalisar Dinkin Duniya su juyawa kasar baya.

Rahotanni sun ce masu zanga zangar na daga cikin magoya bayan sojojin da suka gudanar da juyin mulki a kasar ne.

Sai dai duk da gargadin na Faransa alamu na nuna cewa Sojin na Mali na shirin kawar da kai wajen dakko sojojin hayar na kamfanin Wagner daga Rasha don taimaka mata a yaki da ‘yan ta’addan da suka addabi kasar.

Sojin hayar na Wagner dai sun taimaka a yakin kasashe irinsu Syria da Libya yayinda yanzu haka suke taimakawa a yakin da jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ke yi da ‘yan tawaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *